AFCON:Toure ya ji dadin daukar kofi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ivory Coast wins AFCON 2015 trophy

Dan wasan tsakiya na Manchester City, Yaya Toure ya bayyana daukar kofin gasar zakarun nahiyar Afirka da kasarsa ta Ivory Coast ta yi, bayan ta doke Ghana a cin daga-kai-sai-mai-tsaron-gida, da wani abun al'ajabi.

Mai tsaron gidan Ivory Coast, Boubakar Barry, shi ne ya zura kwallo ta tara wadda ta basu nasara a kan Ghana.

Ivory Coast ta zura kwallaye tara a ragar Ghana, a inda ita kuma Ghana ta zura kwallaye takwas aragar Ivory Coast din, a bugun fanaret bayan dukkannin kasashen biyu sun kasa cin juna a karin-lokacin tantance gwani, ranar Lahadi.

Toure wanda kulob dinsa na Manchester City ya dauki kofin Premier League a bara, ya ce "Idan kulob dinka ya ci wasa, abin farin ciki ne, amma idan kasarka ta ci wasa, abin a yi murna ne."