Diarra yana dab da koma wa West Ham

Image caption Lassana Diarra zai koma West Ham

Tsohon dan wasan tsakiya na Real Madrid, Lassana Diarra yana atasaye da kulob din West Ham kuma gab yake da ya soma taka leda da kungiyar.

Diarra mai shekaru 29, dan kasar Faransa ya dade ba shi da kungiyar wasa tun lokacin da ya bar Lokomotiv Moscow a watan Agustan 2014.

Manajan West Ham, Sam Allardyce ya ce "Yanzu yana atasaye a wurinmu, Kuma gab yake da dawo wa wurinmu."

Nan da kwanaki goma ake tunanin dan wasan zai rattaba hannu a kan yarjejeniyar taka leda a Upton Park.