'Yan takara hudu ne za su nemi shugabancin Fifa

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta bayyana sunayen mutane hudu a matsayin wadanda za su yi takarar shugabancinta a zaben da za a yi a watan Mayu.

Hukumar -- wacce zarge-zargen cin hanci da rashawa suka yi wa katutu -- ta ce ta tantance shugabanta mai-ci, Sepp Blatter, wanda ke son sake yin shugabancinta a karo na biyar, domin ya yi takara.

Sauran mutanen da Fifa ta tantance su ne Yarima Ali bin Al Hussein na kasar Jordan, da tsohon dan wasan Portugal, Luis Figo, da shugaban hukumar kwallon kafar Netherlands, Michael van Praag.

Ana ta yin kiraye-kiraye a kawo sauyi ga hukumar ta FIFA bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa sun mamaye ta sakamakon neman kasar da za ta dauki nauyin gudanar da Gasar kwallon kafar duniya a shekarar 2022.