AFCON:An karrama 'yan wasan Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ivory Coast ta karrama 'yan wasanta

Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya ba wa kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar kyautar kudi har dala miliyan 3.4 bisa nasarar samun lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Daga cikin kudin, kocin kungiyar Herve Renard, ya samu dala 129,000 a inda kowanne daga cikin 'yan wasan 23 suka samu kyautar gida wadda kudinsa ya kai dala 52,000 sannan kuma sun sami karin kudi na dala 52,000.

Ita kuma hukumar wasan kwallon kafa ta kasar ta samu dala 429,000 sannan kuma an ba wa masu ba da shawara ga kungiyar wasan dala 520,000.

An kuma karrama dukkannin 'yan wasan da lambar girma ta kasar.