Van Gaal ya mayar wa Allardyce martani

Hakkin mallakar hoto
Image caption van Gaal ya mayar da martani

Manajan kulob din Manchester United, Louis van Gaal ya mayar wa da kociyan West Ham, Sam Allardyce martani, bisa zargin yin zari-ruga a lokacin wasan kungiyoyin da suka tashi kunnen doki, a Upton Park.

Van Gaal dai ya yi amfani da taswirar filin wasa, a inda yake yi wa 'yan jarida bayani.

Ya ce "Ku yi duba ga wannan bayanin domin ganin yadda muka buga kwallo a filin wasa, wanda tafi karfin dan gaba ma ya samu har ya je ya zura a raga."

Manajan West Ham Allardyce dai ya bayyana sakamakon wasan tsakanin Manchester ta samu a kansu da sakamakon buga kwallon zari-ruga, al'amarin da van Gaal din ya karyata.