JS Kabylie ta yi nasarar daukaka kara

Albert Ebosse Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daga baya an yi bincike da aka ce ba jifa bane ya kashe dan kwallon

Kungiyar kwallon kafa ta JS Kabylie ta yi nasarar daukaka kara kan batun haramta mata shiga wasannin Afirka tsawon shekaru biyu.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ce ta yanke hukuncin dakatar da ita sakamakon mutuwar Albert Ebosse da ya yi a filin wasa.

Dan wasan dan kasar Kamaru ya mutu ne bayan da ya ji mummunan rauni a kansa lokacin da aka kammala wasa a cikin watan Agustan bara.

Kotun daukaka karar wasanni ta ce ta soke hukuncin da CAF ta yanke a cikin watan Oktoba ba tare da bata lokaci ba.

Kotun ta ce CAF ba ta bi ka'idojin da aka tanada idan za a hukunta kulob ba, kuma ba a saurari ba'asin kungiyar da ake tuhuma ba, kafin yanke hukuncin.