Leicester ba ta da niyyar korata — Pearson

Nigel Pearson Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Leicester tana matsayi na 20 na karshe a teburin Premier

Kocin Leicester City Nigel Pearson ya ce kulob din ba shi da niyyar ya kore shi duk da rade radin cewar sun raba gari ranar Lahadi.

Leicester ya bayar da sanarwar cewar bai salllami kociyan mai shekaru 51 daga aiki ba.

Pearson ya ce "har yanzu da sauran shan ruwa na a kulob din", bayan da Arsenal ta doke su 2-1 a gasar Premier a Emirates.

Haka kuma ya kara da cewar duk da suna matsayi na karshe a teburin Premier, yana da jituwa mai karfi tsakaninsa da mahukuntan kulob din.