FIFA rankings: Ivory Coast ta kara samun matsayi

Ivory Coast Team
Image caption Karo na biyu kenan Ivory Coast tana lashe kofin Afirka

Ivory Coast ta dare mataki na biyu a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka, bayan da ta lashe kofin bana.

Haka kuma kasar ta koma matsayi na 20 a jerin kasashen da suka fi iya murza leda a duniya.

Har yanzu Algeria ce a mataki na daya a Afirka, kuma ta 18 a jerin wadan da suka yi fice a iya kwallo a duniya.

Ghana wacce aka doke a wasan karshe a kofin Afirka ta matsa sama zuwa mataki na 25 a duniya.

Jamus wacce ta dauki kofin duniya a Brazil a shekarar 2014, tana matakinta na daya a duniya, a inda Argentina da Colombia da Belgium da kuma Netherlands ke biye da ita.

Ga jerin kasashe 10 da suka fi iya taka leda a Afirka:

1. Algeria

2. Ivory Coast

3. Ghana

4. Tunisia

5. Cape Verde

6. Senegal

7. Nigeria

8. Guinea

9. Cameroon

10. Congo DR

Ga jerin kasashe 10 da suka fi iya murza leda a duniya:

1. Germany

2. Argentina

3. Colombia

4. Belgium

5. Netherlands

6. Brazil

7. Portugal

8. France

9. Uruguay

10. Spain