QPR ya nada Ramsey kocin rikon kwarya

Chris Ramsey Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption QPR tana mataki na 17 a teburin Premier bana

QPR ya bai wa Chris Ramsey matsayin kociyan kulob din har zuwa karshen kakar wasan Premier bana.

Ramsey, mai shekaru 52, shi ne yake jagorantar kulob din wasannin Premier tare da darakta Les Ferdinand, tun lokacin da Harry Rednaff ya yi ritaya.

Tun farko QPR ya tuntubi Tim Sherwood idan zai horar da kulob din, kafin daga baya su kasa cimma matsaya kan kwantiragi.

Haka shima kociyan Derby Steve McClaren da Paul Clement mataimakin kociyan Real Madrid sun yi jawarcin aikin horar da kulob din.