Za a yi bincike kan raunin Gerrard

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Gerrard ya ji rauni ne a wasan da suka doke Tottenham 3-2

Likitoci za su dauki hoton cinyar Steven Gerrard domin duba yanayin raunin da ya ji.

Kyaftin din na Liverpool ya ji ranin ne a wasan da suka doke Tottenham da ci 3-2.

Wannan labarai dai ya sanya watakila dan wasan, mai shekaru 34, ba zai taka leda ba a wasan da za su yi da Crystal Palace ranar Asabar na cin kofin FA.

Gerrard na cikin manyan 'yan wasan da Liverpool ke takama da su.