Premier: FA ta tuhumi Chelsea da Everton

Hakkin mallakar hoto mike hewit
Image caption 'Yan wasan kulob din biyu sun yi fada a filin wasa

Hukumar kwallon kafar Ingila, FA ta tuhumi kulob din Chelsea da Everton saboda rashin tsawatarwa 'yan wasansu.

'Yan wasan kulob din biyu sun yi fada ne a filin wasa lokacin karawar da suka yi, wadda Chelsea ta doke Everton da ci 1-0.

Sai dai dan wasan Chelsea, Branislav Ivanovic, ba zai fuskanci karin hukunci ba saboda fadan da ya yi da dan wasan Everton James McCarthy a mintuna 86 da fara wasan.

An yi cece-kuce lokacin da aka kori dan wasan Everton, Gareth Barry, daga filin wasa bayan da a karo na biyu ya hankade Willian.

Bayan an tashi daga wasan, kociyan Everton, Roberto Martinez, ya ce ya kamata da tuntuni an kori dan wasan na Chelsea daga filin wasa.