Kofin FA: Arsenal ta doke Middlesbrough

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Golan Boro Tomas Mejias ya yi kokari sosai duk da kwallaye biyun da aka jefa ragarsa

Arsenal mai rike da kofin FA ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar cin kofin na hukumar kwallon kafa ta Ingila bayan da ta doke Middlesbrough 2-0.

Olivier Giroud ne ya sa Arsenal ta kawo karshen nasarar da Middlesbrough din ke samu sau shida a jere, inda ya fara jefa kwallon farko a raga minti 27 da shiga fili.

Haka kuma minti biyu tsakani Bafaranshen ya kara kwallo ta biyu a ragar bakin na Arsenal.

Arsenal wadda ta kawo karshen kamfar kofi ta shekara tara da nasarar da ta samu ta daukar kofin na FA a bara, ta kai wasan na dab da na kusa da karshe a matsayin daya daga cikin kungiyoyin Premier biyar da suka kai matakin.

Kungiyar Preston North End ta gasar League One za ta hadu da Manchester United ranar Litinin.

Sabon dan wasan baya na Arsenal Gabriel Paulista, wanda ta sayo daga Villareal a kan fan miliyan 11.2 a watan Janairu ya buga wasan a karon farko.

Bradford da Sunderland

Itama kungiyar Bradford ta kai wasan na dab da na kusa da karshe na gasar cin kofin na FA inda ta doke Sunderland 2-0.

Kungiyar ta Bradford ta nuna cewa nasarar da ta samu a kan Chelsea ta yi waje da ita daga gasar ba wai sammatsi ba ne, inda ta fara zura kwallo a ragar Sunderland din da John O'shea ya ci kansu a minti uku da fara wasa.

Sai kuma can a minti na 64 Jon Stead ya ci gaba da kokarinsa na jefa kwallo a raga a kowane zagaye na gasar, ya ci kwallo ta biyu.

Da wannan nasara Bradford ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar FA, a karon farko tun 1976.