Aston Villa ta fitar da Leicester da 2-1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Leicester ta samu dama sosai kafin a tafi hutun rabin lokaci amma ba ta ci ba

Aston Villa ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, bayan da ta doke Leicester da ci 2-1.

Kungiyar ta yi nasara ne akan takwararta ta Leicester da ci biyu da daya a Leicester City.

Leondro Bacuna ne ya fara ci wa Aston Villa kwallonta a minti na 68, sai kuma Scott Sinclair ya kara ta biyu a minti na 89, kafin Andrej Kramaric ya jefa wa Leicester kwallonta daya bayan mintina 90.

Aston Villa ta samu wannan nasara ne bisa jagorancin sabon kociyanta Tim Sherwood.