Kolo Toure ya yi ritaya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kolo Toure yana cikin 'yan wasan Arsenal da suka dauki Premier a 2003/4 ba tare da an ci su ba

Dan wasan baya na kungiyar Liverpool, Kolo Toure, ya tabbatar da cewa ya yi ritaya daga buga wa kasarsa Ivory Coast wasa.

Dan wasan mai shekaru 33 ya bayyana hakan ne mako daya bayan ya taimaka wa kasar daukar kofin Afrika.

Toure wanda ya fara buga wa Ivory Coast wasa a karawa da Rwanda a watan Afrilu na 2000, ya yi dukkanin wasanni shida da kasar ta yi ta dauki kofin Afrikanta na biyu, bayan bugun fanareti da Ghana da aka tashi da ci 9-8.

Dan wasan ya ce, ''ina kaunar kasata kuma musamman ma a wasan kwallon kafa, to amma fa dole ne a wani lokaci ka tsaya.''

Ya ce, ''burina shi ne na dauki kofin Afrika, amma wannan mataki fa ba abu ne mai sauki ba.''

Toure ya na cikin tawagar 'yan wasan Ivory Coast ta wasan kofin duniya a 2006 da 2010 da 2014.

Haka kuma ya yi wa kasar wasannin gasar kofin Afrika bakwai, inda suka yi rashin nasara a wasannin karshe biyu a fanareti, da Masar a 2006 kuma da Zambia a 2012.

Kolo Toure, ya kuma gabatar da Oumane Viera Diarrassouba a matsayin magajin shi na jagoran 'yan wasan baya na Ivory Coast, wanda ya ce shi kuma zai reni Eric Bailly da Wilfried Kanon.

Toure ya fara wasansa a ASEC Mimosa ta Abidjan,kafin ya tafi Arsenal a 2002 sannan ya koma Man City a 2009 kafin ya je Liverpool a bara.