Usain Bolt zai yi ritaya a 2017

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Usain Bolt ya ce, ''a rayuwata komai mai yuwuwa ne''

Zakaran wasan tseren duniya na Jamaica, Usain Bolt, ya ce zai bar wasan bayan gasar duniya da za a yi a London a 2017.

Dan tseren, mai shekara 28, wanda sau shida yana cin lambar zinariya a wasannin Olympics, ya ce zai mayar da hankali ne a kan tseren mita 100 kawai a 2017 din.

Da farko Bolt ya ce gasar da za a yi a Rio a 2016, ita za ta kasance ta karshe da zai yi, amma yanzu ya sauya shawara, kamar yadda ya bayyana wa jaridar Daily Mail.

Ya ce, ''wannan shi ne kudirina da farko, amma kuma mai daukar nauyi na ya bukace ni da na kara shekara daya, zuwa 2017.''

Babbar gasar da ke gaban Bolt a wannan shekara ta 2015, ita ce gasar duniya da za a yi a birnin Beijin na China daga 22 zuwa 30 ga watan Agusta, inda zai yi kokarin kara wata lambar zinariyar ta duniya akan takwas din ya ci a baya.

Haka kuma yana fatan sauya bajintar da ya kafa ta kammala tseren mita 100 cikin dakika 9.58 a Berlin a 2009.