U17: Ivory Coast da Afrika ta Kudu 2-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe hudu ne daga gasar ta Afrika za su je ta duniya a Chile

'Yan wasan Ivory Coast da na Afrika ta Kudu sun yi 2-2 a gasar cin kofin Afrika na kwallon kafa na matasa 'yan kasa da shekara 17 da ake yi a birnin Yamai na Nijar.

Ivory Coast ta fara cin kwallayenta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, bayan an dawo kuma sai Afrika ta Kudu ta rama.

A daren nan ne na Litinin kuma Mali za ta kara da Kamaru a wasan na rukuni na biyu (Group B).

Ranar Lahadi aka fara gasar ta goma sha daya, wadda Nijar ke karbar bakunci, inda najeriya ta ci Nijar din 2-0.