Ina son sayen dan wasan tsakiya — Van Gaal

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Van Gaal ya ce yana bukatar dan wasan tsakiyar da zai taimaka wa Januzaj da Di Maria

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal, ya tabbatar da cewa yana son sayen dan wasan tsakiya idan aka bude kasuwar sayen 'yan wasa ta bazara.

Van Gaal yana shan suka saboda sanya dan wasan gaba, Wayne Rooney, a gurbin 'yan wasan tsakiya.

A lokacin da aka tambaye shi, shin sayen dan wasan tsakiya shi ne abin da zai bai wa muhimmanci? Sai ya ce "tabbas haka ne".

Van Gaal yana magana ne gabanin fafatawar da za su yi da st Preston North End a gasar cin Kofin FA ranar Litinin.

Ya kara da cewa, "Ina nema yadda zan daidaita 'yan wasa; kuma ina bukatar yin haka ta hanya samun dan wasan tsakiya. Idan na sanya Adnan Januzaj da Angel Di Maria a tsakiya, to akwai bukatar a samu wani dan wasa mai kwazo da zai taimaka musu".