Sacchi: Ba na nuna wariyar launin fata

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sacchi, ya ce, ''ba a fahimci abin da nake nufi ba''

Tsohon kociyan AC Milan da Italiya Arrigo Sacchi ya musanta cewa shi mai nuna wariyar launin fata ne bayan da ya yi korafi da yawan bakar fata a kwallon matasa a Italiya.

Sacchi mai shekara 68, ya yi suka da yadda aka samu yawan 'yan wasa bakar fata a matakin gasar matasa na Italiya.

Ya ce, ''magana ce ta batun kasuwanci, babu ta yadda za ka yi kungiya da za ta kunshi 'yan wasa na waje har 15.''

Sai dai daga baya ya ce, shi kawai yana nufin ya ankarar da cewa kasar tana neman rasa kima da tarihi da kuma alfaharinta ne.

Da aka tambaye shi ya fayyace abin da yake nufi, Sacchi ya ce,''an yi min mummunar fahimta, ka na jin ni mai nuna wariyar launin fata ne?

Ka duba tarihina, na horad da kungiyoyi masu 'yan wasa jinsi daban-daban da suka yi nasara a Milan da Madrid.''

Sacchi ya halarci wajen bikin Viareggio, wanda shi ne mafi armashi na wasan matasa a Italiya, inda ya ga yawan matasan na kasashen waje.

Sacchi ya dauki kofin Turai sau biyu a jere tare da Milan a 1989 da 1990 tare da tsoffin zaratan 'yan wasan nan uku na Holland, Frank Rijkaard da Ruud Gullit da Marco van Basten.

Haka kuma shi ne kociyan Italiya lokacin da ta zo ta biyu a gasar kofin Duniya ta 1994, kuma shi ne darektan wasanni na Real Madrid shekaru goma da suka wuce.