Ciwon ido ya tilasta Purdy ya bar dambe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karon da Purdy ya yi da Kell Brook shi ne fitaccen dambensa

Tsohon zakaran damben boksin na ajin matsakaita nauyi na Birtaniya, Lee Purdy ya yi ritaya bayan da ya samu matsala a idonsa na hagu.

Dan damben mai shekaru 27, ya ji rauni ne a damben da Leonard Bundu ya doke shi, a watan Disamba na 2013.

A turmi (round) na bakwai ne mai koyar da Purdy, ya nemi a dakatar da damben a karawar tasa da Bundu zakaran duniya na IBF.

Bayan aikin da aka yi ta yi masa a idon daga karshe dai ya yanke shawara ya bar wasan damben.

A damben da ya yi gaba daya Lee Purdy, ya yi nasara a guda 20, an doke shi sau biyar, sannan ya yi canjaras sau daya.