Jadawalin gasar Premier ta Najeriya

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Page
Image caption Kano Pillars na wakiltar Najeriya a gasar kofin zakarun Afrika

Zakarun gasar Premier ta Najeriya, Kano Pillars za su fara wasan kare kambinsu da wasa a waje da kungiyar Heartland ta Owerri.

Hakan na kunshe ne a jadawalin gasar ta Premier ta kakar 2014/15 wadda aka fitar a Abuja ranar Laraba.

Kungiyar Eyimba wadda ta zo ta biyu a bara za ta fara wasanta ne a gida tare da Akwa United FC.

Sabbin kungiyoyin da suka dawo gasar ta Premier a bana Kwara United da Shooting Stars za su yi wasanninsu na farko a waje.

Kwara United za ta je gidan Dolphins, yayin da Shooting Stars za ta ziyarci Wikki Tourist.

Jadawalin gasar ta Premier na banan ya nuna cewa za afara wasannin ne a ranukan bakwai da takwas na watan Maris.

Ga sauran wasannin satin farko;

El-Kanemi Warriors da Nasarawa United; Sharks da Sunshine Stars; Giwa FC da Abia Warriors; Bayelsa United da Lobi Stars; Gabros da Warri Wolves; Taraba da Rangers