Mourinho ya kasa jure wa matsin lamba a Real

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho ya fuskanci matsi a Real Madrid

Tsohon shugaban kungiyar Real Madrid, Ramon Calderon ya ce Jose Mourinho ya kasa jure wa matsin lambar jan ragamar Real.

Mourinho ya jagoranci Real Madrid daga shekara ta 2010 zuwa 2013, inda ya lashe gasar gasar La Liga a shekara ta 2012 da kuma kofin Copa del Rey a 2011 kafin ya koma Chelsea.

Calderon ya ce "Kasancewa manajan Real Madrid na da matukar wuya, dubi abin da ya rasu da Mourinho."

Mourinho ya kasance na biyu a kakar wasa ta farko a Madrid kafin ya lashe kofin a kakar wasa mai zuwa.

Ya lashe gasar zakarun turai tare da Porto da Inter Milan.