Premier:Everton ta kasa nasara a gida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lukaku ya samu damar cin kwallaye amma ko daya bai ci ba

A cigaba da wasannin Premier na sati na 26, na ranar Lahadi, Tottenham da West Ham sun yi 2-2, kamar yadda Everton da Leicester suka tashi, yayin da Liverpool ta doke Southampton 2-0.

West Ham ce ta fara cin kwallayenta biyu ta hannun Diafra Sakho da Cheikhou Kouyate, kafin Tottenham ta rama.

Da wannan sakamakon Tottenham tana matsayin ta bakwai da maki 44, maki uku tsakaninta da mai matsayi na hudu wato Manchester United.

Ita kuwa kungiyar Everton wadda ita ma ta yi 2-2 da Leicester, hakan na nufin ta yi canjaras a wasanninta bakwai daga cikin 13 na gida, inda ta yi nasara a uku kawai.

Kungiyar wadda rabonta da nasara a gida tun ranar 15 ga watan Disamba, da wannan sakamako, tana matsayi na 12 a tebur da maki 28.

Ita kuwa Leicester tana matsayin ta karshen tebur, wato ta 20 da maki 18.

Liverpool kuwa ta bi Southampton ne har gida ta doke ta da ci 2-0, abin da ya matsar da ita zuwa matsayi na shida da maki 45.

Coutinho ne ya fara jefa mata kwallo a raga minti uku kacal da shiga fili, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma sai Sterling ya kara ta biyu a minti na 73, nasarar da zama ta hudu a jere da klub din ke samu.

Southampton wadda ta yi rashin nasara a wasanni uku cikin biyar ita ce ta biyar da maki 46., yayin da Liverpool din ta ci gaba da kasance wa a matsayin kungiyar da ba doke ba har a yanzu a Premier a bana.