Tennis: Murray ya kawar da Nadal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne matsayi mafi girma da ya kai tun 2013

Andy Murray ya kawar da Rafeal Nadal daga matsayin na uku a duniya a kwallon tennis.

Murray dan yankin Scotland, mai shekara 27 ya kai wannan matsayin mafi girma ne, tun bayan da ya zama na biyu lokacin da ya yi nasara akan Novak Djokovic a wasan karshe na Wimbledon a 2013.

A watan Satumba na 2014, ya dawo na 12 bayan ya bar wasanni tsawon watanni uku saboda jinyar ciwon baya.

Djokovic dan Serbia, ya ci gaba da rike matsayinsa na daya a duniya, kamar yadda Roger Federer na Switzerland ya ke rike da matsayi na biyu, sai Murray din sannan kuma Nadal yanzu ya dawo na hudu.

A wannan makon Murray zai yi wasa da Gilles Muller dan kasar Luxembourg a zagayen farko na gasar Dubai.