QPR ta kaura zuwa Dubai

Hakkin mallakar hoto qpr
Image caption Sabon filin wasan kungiyar QPR

Kungiyar QPR ta Premier ta tafi Dubai domin atisaye saboda matsalar tsananin sanyi da ruwa da ya kwanta a filinta.

Saboda Tottenham da za ta hadu da su ranar Lahadi, za ta kara da Chelsea a wasan karshe na kofin Capital One, aka daga wasan nasu na Premier, zuwa Asabar ta sama

Kuma sakamakon ruwan sama da ya mamaye filin atisayensu na Kwalejin Imperial da kuma tsananin sanyi, ya sa suka tafi Dubai ranar Litinin domin tsara yadda za su fuskanci sauran wasanninsu 12 da suka rage, inda za su dawo ranar Asabar, inji kociyansu Chris Ramsey.

Wasan kungiyar ta QPR na gaba yanzu shi ne, wanda Arsenal za ta zo mata gida ranar Laraba hudu ga watan Maris.

Kungiyoyin Newcastle da Stoke da Manchester City dukkaninsu sun je Dubai domin atisaye a shekaran nan ta 2015.

Kwana daya da dawowar zakarun Premier Manchester City daga Dubai din ne Middlesbrough ta gasar kasa da Premier ta Championship, ta fitar da su daga gasar kofin FA.