Cristiano Ronaldo: ya shiga tarihi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kididdigar ta Ronaldo ta fara ne daga 2009 zuwa yanzu

Cristiano Ronaldo ya zama na uku na jerin wadanda suka fi ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi, bayan wasan La Liga da suka yi nasara akan Elche.

Kwallon da dan wasan na Portugal ya ci Elche, ita ce ta 290 da ya ci wa Real Madrid, a wasan da suka tashi 2-0 ranar Lahadi.

Hakan ya sa ya wuce Carlos Santillana, kuma kwallo 33 suka rage masa ya kamo bajintar Raul mai kwallaye 323 a tarihin kungiyar.

Ita dai Real Madrid tun a wasanta da Schalke na kofin Zakarun Turai ranar 18 ga watan Fabrairu, ta ce Ronaldo ya kai bajintar cin kwallo ta 290.

To amma hukumar La Liga ta bayar da wata kwallo da kungiyar ta ce Cristiano ne ya ci, a wasansu da Real Sociedad a watan Satumba na 2010 ga Pepe shi ma dan Portugal