Enrique: Barca da Man City ba gwani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption ''Sai mun tashi tsaye mu nuna cewa mun fi Man City''

Kociyan Barcelona Luis Enrique ya ce babu kungiyar da za a ce kai tsaye za ta yi nasara a karawar da za a yi tsakanin kungiyarsa da Manchester City, ranar Talatar nan a Etihad.

Tshohon dan wasan dan kasar Spaniya ya ce, ba za a tabbatar da cewa Barcelona za ta doke Man City ta kai wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai ba.

Enrique ya ce abu ne mai hadari ka fitar da kungiya da cewa ta fi wata a gasar Zakarun Turai, sai dai ka nuna iyawarka kawai a filin wasa.

Barca na neman zuwa wasan dab da na kusa da karshe ne a karo na takwas a jere, ita kuwa Man City ba ta taba zuwa matakin ba.

Kungiyar ta Spaniya ta doke zakarun na Premier a haduwarsu ta bara da ci 4-1 wasan gida da waje.