Kofin Afrika: Fifa ta sauya lokaci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Fifa ta sanar da sauyin maimakon hukumar CAF

Fifa ta sauya lokacin gasar Kofin kwallon kafar Afrika ta kasashe ta 2023 da za a yi a Guinea zuwa watan Yuni, domin gasar kofin Duniya ta 2022 a Qatar.

Hukumar ta kwallon kafa ta duniya ta sauya lokacin gasar ne da aka saba yi a watannin Janairu da Fabrairu saboda gasar duniya.

Fifa ta tsara za a yi gasar ta duniya ne a tsakanin watan Nuwamba da Disamba na 2022 domin kaucewa yin gasar a lokacin zafi.

Babban Sakataren Fifa, Jerome Valcke shi ne ya sanar da sauyin na gasar ta Afrika a Qatar.