Fifa ta wanke D'Hooghe kan cin hanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwamitin ya wanke Michel D'Hooghe daga zargin laifuka hudu

An wanke dan kwamitin zartarwa na, Fifa, Michel D'Hooghe kan zargin cin hanci na karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 da ta 2022.

Kwamitin da'a na hukumar kwallon kafar ta duniya, ya ce, bai samu isassun shedu da suka nuna D'Hooghe, mai shekara 69 ya saba ka'idojin aikinsa ba.

Jami'in dan kasar Belgium, wanda shi ne shugaban kwamitin lafiya na Fifa, wanda kuma ke kwamitin zartarwar hukumar tun 1988 ya musanta aikata wani laifi.

Rasha aka bai wa damar gudanar da gasar cin Kofin Duniya ta 2018, yayin da Qatar ta samu ta 2022.