''Fanaretin Messi ta ba mu kwarin guiwa''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hart ya fadi bangaren hagu kamar yad da sauran gololin da suka kade fanaretin Messi 7 suka yi

Kociyan Manchester City Manuel Pellegrini yana ganin fanaretin Messi da golansu ya kade ta ba su kwarin guiwar cigaba a gasar Kofin Zakarun Turai.

Kociyan ya ce, ''abu ne mai muhimmanci a garemu, domin da zai yi wuya sosai mu iya wani abu idan da 3-1 aka ci mu.''

Pellegrini, da kasar Chile, ya ce ko da ike ba abu ne mai kyau ba a doke ka a gida, amma za mu je Barcelona mu yi kokarin nasara, domin muna da damar hakan.

Shi kuwa kociyan Barcelona Luis Enrique ya ki sukan Messi, wanda ya ci fanareti 44 daga cikin 57 da ya buga wa Barcelona, kan barar da fanaretin ranar Talata.

Kociyan dan Spaniya, ya ce, '' 'yan wasan da suke buga fanareti, sukan yi rashin sa'a a wasu lokutan, amma mu muna da kwarin guiwa sosai akan Messi.''

Manchester City na bukatar ta ci akalla kwallaye biyu a Nou Camp a haduwarsu ta biyu da Barcelona don zuwa wasan dab da na kusa da karshe na gasar.