Wariya: An yi wa Steau Bucharest hukunci

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Magoya bayan Staeua Bucharest ke nan na amfani da tartsatsin wuta a filin wasa

Uefa ta umarci Steaua Bucharest ta yi wasanninta biyu na gida na gasar kofin Turai na gaba ba tare da 'yan kallo ba saboda laifin wariyar launin fata da magoya bayanta suka yi.

Magoya bayan kungiyar sun daga wani kyalle ne mai rubutun wariyar launin fata a lokacin wasansu na Kofin Europa da Dynamo Kiev a Bucharest a watan Disamba.

Hukumar kwallon kafar ta Turai ta yi wa kungiyar ta kasar Romania hukuncin ne saboda aikata laifin a karo na uku a bana.

Haka kuma kungiyar za ta biya tarar fan 14,668 kan wasu laifuka biyu, da magoya bayan nata suka yi, na amfani da tartsatsin wuta da cocilan mai hasken tsiya a lokacin wasa.

Kasancewar an fitar da kungiyar a gasar Kofin Europa a matakin kungiyoyi a bana, hukuncin zai tabbata ne a kakar wasanni mai zuwa.