Damben Frampton da Avalos

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ina son in zama gagararre a kowana dambe- Frampton

Mai rike da kambun duniya na ajin karamin nauyi na damben boksin na IBF Carl Frampton ya ce, yana sa ran doke mai kalubalantarsa Chris Avalos cikin sauki ranar Asabar.

A ranar Asabar za a yi karawar a filin Odyssey Arena da ke Belfast, babban birnin Ireland ta Arewa.

Frampton mai shekara 28, wanda ba a taba buge shi ba, ya kwace kambun ne daga Kiko Martinez a watan Satumba da yawan maki.

Kafin damben nasa na farko na kare kambun, Zakaran ya ce, ''idan na je damben zan yi nasara ne kawai.''

Ya ce, ''ina son na ci gaba da samun nasara kuma na zama gagarabadau a kowane dambe, na san yana da karfin hali amma zan doke shi.''

Mai kalubalantar ta sa, Chris Avalos, ya doke Yasutaka Ishimoto a watan Mayu ne ya samu matsayin kalubalen.