Dortmund: An gano bam a filn wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasan yana daukar mutane 80, 720

An gano wani bam da bai fashe na tun lokacin yakin duniya na biyu a kusa da filin wasan kungiyar Borussia Dortmund.

Bam din wanda kafar yada labarai ta Jamus, DW ta bayar da rahotan gano shi ranar Alhamis, kirar Birtaniya ne.

A yanzu dai ana shirye-shiryen kwance shi, yayin da aka kaurace wa harabar filin wasan.

Gano irin wadannan bama-bamai ba sabon abu ba ne a Jamus, inda sojin taron-dangi da na Rasha suka jefa miliyoyinsu lokacin yakin duniya na biyu a 1939-45.

Birnin na Dortmund ya sha ruwan bama-bamai da suka lalata shi a lokacin.