Kwallon kafa: Girka ta sauya hukunci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabuwar gwamnatin kasar ta lashi takobin kawo karshen rikici a wasan kwallon kafa

Gwamnatin Girka ta sauya shawara kan hukuncin da ta yi na dakatar da wasannin kwallon kafa na kwararru na kasar har sai abin da hali ya yi.

Dakatarwar ta uku a kakar wasanni ta bana, yanzu ta shafi babbar gasar lig din kasar ne wato Greek Super League kadai kuma tsawon mako daya kawai.

Gwamnatin ta dauki matakin dakatarwar ne domin kawo karshe tashe-tashen hankali a wasannin kwallon kafa.

Kuma ta yi hakan ne bayan rikicin da ya barke a wasan babbar gasar kasar tsakanin Olympiakos da Panathinaikos ranar Lahadi.

Sannan kuma da fadan da aka yi tsakanin shugabannin kungiyoyin lokacin wani taro ranar Talata.

A ranar Laraba ne aka sanar cewa an dakatar da dukkanin wasannin kwararru na kasar sai abin da hali ya yi.

Amma bayan taro na biyu da Framinista Alexis Tsipras, mataimakin ministan wasanni Stavros Kontonis ya ce yanzu dakatarwar ta shafi wasan karshen makon nan ne kawai