U17: Mali ta kai wasan karshe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Mali sun samu wannan dama ce a gasar ta 11

Mali ta kai wasan karshe na Kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 17 a Nijar bayan ta doke Guinea 2-1.

A ranar Lahadi, Malin za ta hadu da Afrika ta Kudu a wasan karshe, yayin da Najeriya za ta kara da Guinea a ranar domin matsayi na uku.

Kasashe hudu da suka kai wasan kusa da karshen za su wakilci Afrika a gasar duniya a Chile.

Za a yi a gasar ne daga 17 ga watan Oktoba zuwa takwas ga watan Nuwamba.