An yi wa dan wasa barazana da bindiga kan fanareti

Image caption A wasan Novi Pazar ta sha kashi daya ba ko daya

Magoya bayan wata kungiyar kwallon kafa ta Serbia sun yi wa wani dan wasansu barazana da bindiga saboda ya kasa cin fanareti.

Kwallon da Zarko Udovicic dan wasan baya na kungiyar ta Novi Pazar ya buga ta haure sama ne a babban wasan da su ke da FK Rad a makon da ya wuce.

A minti na 85 ne dan wasan ya barar da damar bayan an ci su daya, haka kuma aka tashi wasan.

Bayan kwana biyu da wasan ne sai wasu mutane, suka shiga, dakunan sanya kaya na filin atisayen kungiyar, suka yi wa dan wasan barazana da bindiga.

Shugaban kungiyar kwararrun 'yan wasan Serbia Mirko Poledica, ya ce abin takaici hukumar kwallon kafa da hukumar gasar lig din kasar ba wadda ta dauki mataki akai.

Ya ce, ''dole ne a dauki matakin kare lafiyar 'yan wasa, amma ba su yi ba. Nan gaba za a iya kashe wani dan wasa.''