Blackett ya sabunta kwantiragi da Man U

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blackett ya taso ne daga makarantar horad da matasan 'yan wasa ta Man United

Dan wasan baya na Manchester United Tyler Blackett ya sabunta kwantiraginsa har zuwa watan Yuni na 2017.

Dan wasan wanda wanda buga wa Man United wasanni goma tun wasansa na farko da Swansea a bana yana da damar tsawaita kwantiragin da shekara daya.

Blackett, ya ce, ''abin ya faranta min rai sosai, ina goyon bayan United duk tsawon rayuwata, burina ya cika da na fara musu wasa bana.

Kociyan kungiyar ta manchester United, Louis van Gaal, ya ce, Blackett zai iya zama wani babban dan wasa nan gaba.