Arsenal ta doke Everton 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nasarar ita ce ta uku a jere da Arsenal ke samu a Premier

Arsenal ta koma ta uku a teburin Premier bayan da ta doke Everton da ci 2-0 a filinta na Emirates.

Olivier Giroud ya saka wa Arsene Wenger da sa shi da ya yi a wasan duk da kwallayen da ya barar a karawarsu da Monaco da ta lallasa su a gasar Zakarun Turai ranar Talata, inda ya ci kwallo a minti na 39.

Romelu Lukaku ya samu damar cin Arsenal amma golansu David Ospina ya hana shi, kafin kuma Tomas Rosicky ya kara kwallo ta biyu a minti na 89.

Maki shida ne tsakanin Everton da ta farko a kungiyoyi uku na karshen teburin Premier, inda take da maki 28, a wasa 27.

Yanzu Arsenal na matsayin ta uku a tebur da maki 51 a wasanni 27, yayin da Manchester United ta dawo ta hudu da maki 50.