Chelsea ta dauki Kofin Capital One

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption John Terry ya ci wa Chelsea kwallon farko da harin farko

Jose Mourinho ya dauki kofinsa na farko tun bayan da ya dawo Chelsea, bayan da kungiyar ta doke Tottenham a gasar kofin League a filin Wembley.

Bayan da Christian Eriksen ya kai wa Chelsea hari, kwallon ta doki saman karfen raga, kyaftin din Chelsea John Terry ya ci kwallon farko a minti na 45.

Sai kuma kwallo ta biyu wadda Diego Costa ya shirgo, dan wasan Tottenham Kyle Walker ya je tarewa ya ci kansu a minti na 56.

Mourinho, wanda ya dawo Stamford Bridge a farkon kakar bara bayan ya je Inter Milan da Real Madrid, yanzu ya jagoranci kungiyar ta dauki kofuna bakwai a kociyanta da ya yi sau biyu.

Dukkanin kungiyoyin biyu sun doke junansu sau dai-dai a kakar bana kafin wannan haduwar tasu.

Rabon Tottenham da daukan kofi tun wanda ta ci na League a 2008.