Liverpool ta nakasa Man City da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawanci Coutinho yana ci wa Liverpool kwallon da ta ke nasara bayan ta farko

Liverpool ta bata wa Manchester City lissafin kare kofinta na Premier da ci 2-1 a Anfield a wasa na mako 27, abin da ya kara ratan da Chelsea ta ba Zakarun Premiern.

Jordan Henderson ne ya fara jefa kwallo a ragar Manchester City ana minti 11 da fara wasa, kafin Edin Dzeko ya rama wa bakin a minti na 25.

Sai dai kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne ana minti 75 da wasa sai dan wasan tsakiya dan Brazil, Coutinho ya kara ci wa Manchester City kwallo ta biyu.

Sakamakon ya sa City tana bayan Chelsea ta daya a tebur, mai maki 65,a wasanni 26, da maki 60 a wasanni 27, yayin da Liverpool din ta zama ta biyar da maki 48, a wasanni 27.

Hakan ya sa Liverpool ta ci gaba da kasance wa kungiyar da ba a doke ta ba a Premier a wannan shekara ta 2015.

A wasanni 13 na baya-bayan nan da Manchester City ke ziyartar Liverpool a Anfield har yanzu ba ta taba nasara a kan masu masaukin nata ba.