Mourinho na neman karin kofuna

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kofin shi ne na 21 da Mourinho ya dauka

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya kudiri aniyar daukar karin kofuna bayan da ya yi nasarar cin na Capital One ranar Lahadi, wanda shi ne na farko a zuwansa Chelsea na biyu.

Kofin shi ne na 21 da kociyan dan kasar Portugal ya dauka a tsawon aikinsa.

Ya ce, '' ji na ke kamar yaron da ya ci kofinsa na farko, abu ne mai wuya gare ni in rayu ba tare da kofi ba, ina bukatar in ciyar da kaina da kofuna.''

Mourinho, wanda ya fara aikin kociyan Chelsea a tsakanin 2004 da 2007 kafin ya sake dawowa a 2013, yanzu ya dauki kofuna bakwai da kungiyar ta London.

Kofinsa na farko a Chelsea shi ne na League a 2005, wanda daga shi kuma ta dauki na Premier a wannan kaka, kuma a yanzu tana kan hanyar maimaita hakan.

Chelsea tana gaban Manchester City ta biyu a Premier da tazarar maki biyar da kuma bashin wasa daya.