Hukumar NFF ta caccaki Stephen Keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Keshi na fuskantar matsi kan Super Eagles

Wani babban jami'in hukumar kwallon Nigeria, NFF Felis Anyansi-Agwu ya soki Stephen Keshi kan batun sabuwar kwangilar da ta ke neman kullawa tare da shi.

Keshi dai ya ce sabuwar kwangilar da aka yi masa tayi tamkar "bauta za a sa shi".

Agwu ya ce bai kamata Keshi ya dunga ba ta sunan hukumar NFF ba, idan yana da korafi ya zo ya gaya mata.

An samu rarrubuwar kawuna tsakanin 'yan Nigeria ko Stpehen Keshi ya cancanci ya ci gaba da jan ragamar Super Eagles ko kuma a'a kasancewar kasar ta kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin Afrika a bana.

Tun daga watan Disambar bara, Daniel Amokaci ne ke jagorantar Super Eagles a matsayin kocin riko.