Ivory Coast: Boubacar Barry ya yi ritaya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sai dai Barry, zai ci gaba da yi wa kungiyarsa ta Belgium Lokeren wasa

Golan Ivory Coast ya yi ritaya daga buga wa kasar wasa kasa da wata daya da ya taimaka mata ta dauki Kofin Afrika.

Barry mai shekara 35, ya taka gagarumar rawa a wasan karshe da kasar ta doke Ghana a bugun fanareti ta dauki kofin ranar 8 ga watan Fabrairu.

Mai tsaron gidan ya kare bugun fanareti biyu kafin ya ci wadda ta ba su damar daukar kofin.

Barry ya yi wa Ivory Coast wasanni 86, kuma ya halarci gasar Kofin Duniya uku- a 2006 da 2010 da kuma 2014.

Haka kuma ya buga gasar cin Kofin Afrika ta 2012 wadda Zambia ta yi galaba a kansu da bugun fanareti.

Barry ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa , ''duk wani abu mai kyau zai kare. Na yanke shawarar kawo karshen buga wa Ivory Coast wasa. Ina alfaharin yi wa kasarmu wasa.''