'Yan wasan Amurka sun bayar da taimakon kwakwalwa

Image caption 'Yan wasan zari-ruga na Amurka da dama sun gamu da matsalar cutar kwakwalwa

Wasu 'yan wasan zari-ruga biyu na Amurka sun ce za su bayar da kwakwalwarsu idan suka mutu domin gudanar da binciken kimiyya.

Dan wasan New York Giants Steve Weatherford da tsohon dan wasan Seattle Seahawks Sidney Rice suna son bayar da gudummawarsu ne wajen bincike kan raunin kwakwalwa.

'Yan wasan zari-ruga na Amurka da dama sun gamu da matsalar cutar kwakwalwa.

Weatherford ya ce akwai matsaloli da dama da ke faruwa sakamakon rauni a kwakwalwa, ba ga 'yan wasa kadai ba, abu ne da yake shafar kowa.

Shi kuwa Rice ya yi ritaya daga wasan a shekarar da ta wuce, yana da shekara 27, saboda lafiyarsa bayan da ya sha duka da dama a kansa a wasan.

'yan wasan biyu sun ce suna fatan shawarar tasu za ta sa wasu ma su taimaka wajen bincike a kan raunin kwakwalwa.

Kusan 'yan wasa 4,500 ne ke karar hukumar kwallon zari-ruga ta Amurka, National Football League,(NFL), saboda raunukan da suka ji a ka lokacin da suke wasan.

A yanzu ma an kusa sasantawa domin biyansu diyyar kusan dala miliyan dubu daya.