Kila a dawo da Micheal Phelps wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Phelps ya ci lambobin zinare 58 da na azurfa 11 da na tagulla uku

Mai yuwuwa a bai wa zakaran wasannin Olympics da ya ci lambar zinare 18 dama ya shiga gasar duniya ta Rasha bayan an haramta mi shi shiga wasanni.

An dakatar da Ba-Amurken mai shekara 29 daga shiga wasanni da duk wata gasa ta duniya tsawon watanni shida bayan da aka same shi da laifin tuki cikin maye.

Darektan hukumar wasan linkaya na Amurka Chuck Wielgus ya ce, ''abu ne mai sarkakiya, barin dan wasan, amma dai akwai hanyoyin da hakan za ta tabbata.''

Ana dai sa ran Phelps zai dawo was a yayin babbar gasar wasanni ta Amurka da za a yi a Arizona a watan Afrilu, idan lokacin dakatarwarsa ya kare.

Da ya sanar da cewa zai yi ritaya bayan gasar London ta 2012, amma ya sauya shawara, inda yanzu ya ke shirya wa gasar Olympics ta 2016 da za a yi a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

Tu ni ya samu cancantar shiga tawagar 'yan wasan linkaya na Amurka na gasar ta duniya da za a yi a birnin Kazan na Rasha daga 24 ga watan Yuli zuwa 9 ga Agusta.

A watan Satumba na 2014 kotu ta samu Michael Phelps da laifin tuki cikin maye a garinsa Baltimore.

Kotun ta yanke masa dagaggen hukuncin zaman gidan yari na shekara daya ta yi masa hukuncin je-ka-ka-gayara-halinka na watanni 18.