Premier: Mourinho ya sa burin maki 91

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mourinho ya ce, ''idan muka ci wasanni goma muka yi canjaras a daya shi ke nan''

Jose Mourinho ya sanya wa Chelsea burin daukar kofin Premier da maki 91 a bana, yayin da ya rage mata wasanni 12 a gasar.

Hakan na nufin suna bukatar maki 31 daga ragowar wasanninsu 12, su yi nasara a goma da canjaras a daya.

A yanzu Chelsea tana matsayi na daya da tazarar maki biyar da kwantan wasanta daya tsakaninta da Manchester City mai maki 55.

Sai dai Mourinho ba ya ma tunanin kungiyar ta yi irin kura-kuran da Man City ta yi a bana kamar yadda Liverpool ta ci su 2-1 ranar Lahadi.

Kociyan ya ce, ''idan masu bin mu a baya suka yi rashin nasara, hakan alheri ne a gare mu.

Muna da tazarar maki biyar, wanda a wannan gasa ba wani abu ne mai yawa ba.''

Ya ce, ''lissafi yana taka rawa a duk wannan, inda wasanni 12 suka rage, da maki 36, idan aka debe maki biyar, muna bukatar 31.