Premier:Chelsea ta ci gaba da jan ragama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Eden Hazard yana zura kwallo ragar West Ham

Chelsea ta ci gaba da bayar da tazara a gasar Premier bayan da ta yi nasara a gidan West Ham United da ci 1-0.

Yanzu tana da maki 63 da kwantan wasa daya, yayin da Man City ke bi mata baya da maki 53, bayan da ita ma ta ci Leicester 2-0.

Arsenal ta ci gaba da kasancewa ta uku da maki 54, yayin da Man United ta ke bin ta da maki 53.

Ga yadda sakamakon wasannin suka kasance, yayin da ya rage wasanni 11 a kammala gasar ta Premier.

QPR 1 - 2 Arsenal ;West Ham United 0 - 1 Chelsea ;Manchester City 2 - 0 Leicester City; Newcastle 0-1Man United

Stoke 2 - 0 Everton;Tottenham 3 - 2 Swansea ;Liverpool 2 - 0 Burnley