Hukumar FA ta Ingila na tuhumar Poyet

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gus Poyet

Hukumar kwallon Ingila, FA na tuhumar kocin Sunderland Gus Poyet sakamakon wasansu da Hull City a ranar Talata.

Tuhumar ta shafi yadda ya yi kwallo da goran ruwa saboda alkalin wasa ya kore shi daga cikin fili.

Tun da farko kocin Hull, Steve Bruce ya kai karar Poyet zuwa hukumar kwallon Ingila, inda ya bukaci a ja kunen Poyet.

Poyet na da damar mayar da martani daga nan zuwa karfe 6 na yamma a ranar Litinin mai zuwa.

An ta shi wasan daya da daya tsakanin Sunderland din da Hull City.