Van Gaal: Ba zan bi magoya baya ba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption ''Tsarin kwallon Ingila ne a rika kai hari ba kakkautawa''

Kociyan Manchester United Luis van Gaal ya ce ba zai mika wuya ga bukatar magoya bayan kungiyar ta kai hari ko da yaushe a wasa maimakon rike kwallo a baya ba.

Kociyan ya ce, ''na yarda da magoya bayan cewa bai zama dole mu yawaita mayar da kwallo wurin golanmu ba, domin akwai yadda za mu yi wasa da zafi-zafi ba tare da amfani da shi ba.

To amma shi kansa mai tsaron ragar dan wasanmu ne na goma sha daya, ta yaya za mu bar shi.''

''Shi kansa golan zai iya zaburad da wasanmu, kuma a wasu lokutan ta De Gea za mu kai wasan gaba.''

Van Gaal ya kara da cewa, ya fahimci cewa tsarin wasan Ingila shi ne a rika kai hari ba kakkautawa.

Ya ce, to amma su kansu magoya bayan kungiyar yana ganin suna jin dadin yadda Manchester ke rike kwallo, a don haka ko da yaushe kokarin hada tsarin biyu ne.

Magoya bayan kungiyar ba su ji dadin yadda aka mayar da wata kwallo ta bugun gefe(kwana), daga bangaren abokan karawarsu ba har zuwa wajen golansu, De Gea, a karawarsu da Sunderland ranar Asabar.

Hakan ya sa magoya bayan suka rika kiran da 'yan wasan su rika kai hari maimakon mayar da kwallo baya.