Fifa: Luis Figo ya yi garaje - Bwalya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Figo ya kaddamar da takarar kalubalantar Blatter

Gawurtaccen dan kwallon Afrika, Kalusha Bwalya ya ce Luis Figo ya garaje wajen neman takarar shugabancin hukumar kwallon duniya, Fifa.

Figo mai shekaru 42 wanda tsohon gwarzon dan kwallon duniya ne, na daga cikin mutane uku uku da ke shirin kalubalantar Sepp Blatter a ranar 29 ga watan Mayu.

"Luis Figo babban dan kwallo ne amma da ya soma ne da shugabantar hukumar kwallon Portugal," in ji Bwalya wanda shi ne shugaban hukumar kwallon Zambia.

Bwalya wanda babban jami'i ne a hukumar kwallon Afrika watau Caf ya kara da cewa "Akwai wasu 'yan wasa kamarsu Davor Suker wanda a yanzu shi ne shugaban kwallon Croatia".

A cewar Bwalya kamata ya yi Figo ya soma daga kasa kafin ya ce zai hau sama.

Bwalya ya kara da cewa tuni wasu hukumomin kwallon kafa suka yanke shawarar wanda za su zaba a kujerar shugabancin Fifa.