U20 : Ghana ta ci Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ghana ce ta daya a rukunin na biyu

Ghana ta doke Afrika ta Kudu da ci 2-0 a gasar kofin Afrika ta 'yan kasa da shekara 20 da ake yi a Senegal.

Minti takwas da fara wasa dan Afrika ta Kudu Mdiba ya ci kansu, kafin dan wasan Ghana Tetteh ya kara ta biyu.

Mali da Zambia su ma a rukuni na biyu (Group B), suna karawa a daren na Litinin.

A ranar Laraba ne za a ci gaba da wasannin rukuni na farko wanda Najeriya da ta ke ta daya za ta kara da Congo, Ivory COast da Senegal